Shugaban ya ce, shi ya bai wa zaratan sojojin kasar umurnin gudanar da binciken da ya gano mutumin da ake zargi mai suna Mustafa al-Imam, sai dai, Trump bai yi karin haske ba a game da irin rawar da wanda ake tuhumar ya taka a harin da ya harzuka Amruka.
Majiyar ta ce yanzu haka ana kan hanyar isar da mutumin da ake zargin a Amurka domin fuskantar hukunci.
Har ila yau shugaban kasar ta Amurka ya kara da cewa, ba za su taba gajiyawa ba, a kokarinsu na gano wadanda suka kitsa harin, domin gurfanar da su a gaban kotu.
Yanzu haka dai, ana yi wa wani dan kasar ta Libiya, Ahmed Abou Khattala, shari’a a birnin Washington, a kan hari, shekaru 3 bayan da wani sojan kundunbalar Amruka ya kama shi, tare da tisa keyarsa ta jirgin ruwa zuwa Amruka.